Kamfanin dillancin labarai “Annashra” ta kasar Masat ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Sameh shukri yana fadar haka a wani hira da ya yi da wata tashar Television na kasar a jiya Asabar.
Ministan ya kara da cewa kasar Masar zata ci gaba da bada hadin kai da kawancen da kasar Amurka take jagoranta wajen yakar kungiyar Daeesh ta hanyar musayar bayanai, amma a fagen daga zata kalubalanci kungiyar ne a arewacin yankin sina na kasar.
Dangane da siyasar kasar Syria kuma Ministan ya ce kasarsa tana goyon bayan tattaunawa tsakanin gwamnati da yan adawar kasar .
Dangane da tattaunawa tsakanin Palasdinawa da HKI kuma Sameh Shukri ya ce tattaunawar tana tafiya kamar yadda aka tsara. ABNA